Daga Ibrahim Da’u Dayi
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa Muhammadu Buhari kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya ce zai dawo kan aikin yada labarai kuma ya zama manomi da zarar gwamnati mai ci ta kare.
Adesina ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook da aka tabbatar a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar manoma ta kasa reshen jihar Edo a ofishin sa.
A cikin sakon mai taken, “Sun ga gobe”Adesina ya ce; “Idan na gama mulki da yardar Allah na yi niyyar komawa bakin aikin yada labarai, kuma na kasance manomi.
Acikin maziyartan Akwai Manoman rogo, kokwamba, abarba, kifi, shanu, da sauran amfanin gona da dabbobi.
Maza da mata da matasa, Sun samu jagorancin shugaban su, mai martaba, Alhaji Bako E. Dogwo, koodineta janar na sarakunan gargajiya na Bassa da jigajigan masu fada aji.
Sauran sun hada da; Gladys Iyore Emuze, Sakatare, Aisha Ugbaja, Justice Agbozuadun, Zinat Shaka, da Yusuf Mohammed.
Daga ƙarshe ƙungiyar ta karramashi tare da bashi Mukami na zama daya daga cikin iyayen kungiyar.