Friday, July 12
Shadow

Bayan Awa 24 da yin Gàrkùwà da magaifiyar Rarara har yanzu ba’a gano inda take ba

Rahotanni sun bayyana cewa, awanni 24 bayan yin garkuwa da mahaifiyar shahararren mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu, Rarara har yanzu, ba’a gano inda take ba.

Kakakin ‘yansandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa an kama mutane 2 da ake zargin suna da hannu a yin garkuwa da mahaifiyar Rarara din amma har yanzu ba’a gano inda take ba.

Daily Trust ta ruwaito cewa ‘yan Bindigar da suka je yin garkuwa da mahaifiyar Rarara sun je ne a kafa tike da muggan makamai suka shiga gidanta suka kamata.

Rahoton yace Bata musu gaddama ba kuma babu wanda ya tunkaresu saboda muggan makaman da suke dauke dasu.

Karanta Wannan  NDLEA ta kama muggan ƙwayoyi na naira biliyan 2.1 a Legas da Fatakwal

Daily Trust tace ta nemi jin ta bakin Rarara amma bata yi nasara ba saboda wayoyinsa duk a kulle kuma an aika masa da sakon waya amma bar bayar da amsa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *