fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Bayan cutar coronavirus Omicron, wata cutar na nan zuwa>>WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya ta gargadi manyan kasashe cewa nau’in Omicron na cutar korona ba zai kasance na karshe da duniya za ta gani ba.

Hukumar ta kuma bukaci a raba alluran riga-kafin ta yadda kowace ƙasa za ta sami isassun alluran.

Wata babbar jami’a kuma kwararriyar likitar cututtuka masu yaɗuwa a Hukumar Lafiyar ta Duniya, Maria van Kerkhove, ta shaida wa BBC cewa ta fusata kan yadda manyan kasashen duniya ke mamaye alluran riga-kafin, lamarin da yasa sauran ƙasashen duniya ba sa samunsu kamar yadda suke bukata:

Maria van Kerkhove Ta ce, “Wannan abin matukar takaici ne cewa duk da duniya na da kwarewar hada wadannan alluran riga-kafin masu inganci matuka, amma saboda rashin tausayi da sanin ya kamata, mun kasa raba su ga masu bukata.”

Sai dai ta ce lokaci bai kure ba ga duniya ta cimma mizanin da Hukumar Lafiyar ta bukaci kowace kasa ta yi wa ‘yan kasarat riga-kafi na kashi saba’in cikin 100 na alummarta zuwa watan Yulin wannan shekarar, amma sai kamfanoni masu hada alluran sun rika sayar wa kasashe matalauta alluran maimakon sayar da su ga kasashe masu karfin tattalin arziki.

Tun shekarar bara, Hukumar Lafiya ta MDD ta fara gargadin manyan kasashen duniya kan halayyar babakeren da suke nunawa, ta hanyar saye kusan dukkan alluran da ke kasuwa saboda kawai suna da karfin tattalin arziki.

Kuma duk da cewa MDD ta samar da wani shiri mai suna COVAX da zai samar wa kasashe matalauta alluran riga-kafin a farashi mai rahusa, wanilokacin ma a kyauta, amma a fili yake cewa tsarin ba zai cimma bukatun kasashen ba.

Tilas kuma Hukumar ta fara duba amincewa da alluran da wasu kasashe kamar China da Rasha da Turkiyya da kuma Iran ke hada wa domin ba sauran kasashe zabi ganin cewa alluran sun fi arha idan aka kwatanta su da wadanda manyan kamfanoni kamar Pfizer da Moderna ke hadawa.

BBChausa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.