fbpx
Saturday, August 20
Shadow

Bayan da aka fara musu irin kisan da sukewa mutane, Shuwagabannin masu garkuwa da mutane 5 a Arewa sun nemi sulhu

Bayan shafe tsawon lokaci suna kashe-kashen da sace-sacen mutane da dukiyoyinsu, gungu-gungu na ‘yan fashin da suka addabi yankunan arewa maso yammacin Najeriya na neman sulhu da jama’ar yankunan.

Tun a watan Nuwambar 2021 rahotanni ke cewa ƙasurgumin ɗan fashin daji Bello Turji na neman sulhu tsakaninsa da jama’ar yankin Shinkafi da Isa da Sabon Birni, kuma a watan Disamba wata wasiƙa ta ɓulla inda a ciki yake jaddada aniyarsa ta neman sulhun.

Wasu bayanai na cewa shugabannin ‘yan fashin fiye da 40 ne ke neman sulhu da jama’ar yankunan da suka addaba.

Sai dai akwai maganganu daban-daban game da dalilan da suka sa suke neman zaman lafiyar a yanzu.

Ga wasu ‘yan fashin daji biyar mafiya gawurta da suka nemi sulhu da mutanen garuruwansu.

Ali Kacalla

Ali Kacalla ƙasurgumin ɗan fashi ne da ke ayyukansa a yankin Dansadau da ke cikin Ƙaramar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.

“Babban jagora ne ƙwarai da gaske, ya kai duk inda ba a tunani,” kamar yadda Wazirin Masarautar Ɗansadau Alhaji Mustapha Umar ya shaida wa BBC Hausa.

Wazirin ya tabbatar da cewa wata tawagar wakilci daga ‘yan fashin ta tuntuɓe su ƙarƙashin jagorancin Ali Kacalla, inda ɓangarorin suka bayyana wa juna sharuɗɗansu da kuma aniyarsu ta zaman lafiya.

“Mun yi sulhu da su kuma idan aka samu wani abu na rashin jin daɗi ko kuma aka saɓa yarjejeniyar da muka yi sukan turo mutane. Mu ma muna yin hakan,” in ji Waziri.

Ya ƙara da cewa dalilin wannan sulhun ya sa su ma ‘yan bindigar kan shigo cikin gari cin kasuwanni.

A watan Disamba da ya gabata ne BBC ta ruwaito cewa Msarautar Dansadau ta yi bikin murnar cika wata ɗaya ba tare da harin ‘yan fashin daji ba.

A lokacin, Alhaji Mustafa ya ce suna tunanin zuwan lokacin bazara ne ya sa suka nemi zaman lafiya.

“Muna addu’a idan da alheri da manufa mai kyau suka yi Allah ya tabbatar mana kuma ya ba mu zama lafiya. Idan sun yi ne da wata manufa Allah ya shige mana gaba, ya yi mana maganinsu,” in ji shi.

Bello Turji

Masani kuma malamin tarihi a Jami’ar Usmanu Danfodiyo Dr. Murtala Ahmad Rufai ya tabbatar da cewa Turji da wasu manyan jagororin ‘yan fashi fiye da 40 na neman zaman lafiya a yanzu.

“Akwai ƙungiyoyin ‘yan bindiga 45 da suke neman sulhun nan,” in ji shi. Ya ƙara da cewa “ba fa ina maganar mutum 45 ba, manyan shugabanni nake magana”.

Cikin wasiƙar da ke ɗauke da sunan Muhammadu Bello Turji, ɗan bindigar ya zargi ‘yan sa-kai da cutar da su sannan ya nemi gwamnati ta soke ayyukansu a matsayin sharaɗin zaman lafiya.

Awwalu Daudawa

Tsohon gawurtaccen ɗan fashi Awwalu Daudawa ya rungumi tsarin afuwa da gwamnatin Jihar Zamfara ta ƙaddamar da zimmar kawo ƙarshen hare-haren.

Cikin wata hira da jaridar Daily Trust a watan Fabarairun 2021, Daudawa ya ce ya ɗauki makamai ne sakamakon “rashin adalci da gwamnati ke yi wa al’ummarsa”.

Awwalu Daudawa ne ya shirya tare da sace ɗaliban sakandaren Kankara fiye da 300 a Jihar Katsina a watan Disamban 2020.

A watan Mayu gwamnatin Zamfara ta ba da sanarwar kashe Daudawa sakamakon rikici tsakaninsa da wani gungun ‘yan fashi abokan gabarsa.

Halilu

Gawurtaccen ɗn fashi da ake kira Halilu ma ya bi sahun masu neman sulhun.

Halilu na gudanar da nasa ayyukan fashi da makami a yankin Sububu na Jihar Zamfara, a cewar Murtala Ahmad.

A watan Agusta rundunar sojan Najeriya ta ce ta kai hare-hare a Dajin Sububu, inda ta hari sansanin Halilu a dajin.

PR Nigeria ta ruwaito wani jami’in rundunar na cewa sun kashe ‘yan fashi 45 yayin harin na ranar 6 ga watan Agusta. Sai dai hari bai shafi jagoran ba.

Ɗanƙarami

“Turji ba zai haɗa kansa da Turji ba (wajen rashin imani), ta’addanci tsantsarsa, ko da ido ka gan shi, sai Ɗanƙarami,” kamar yadda Murtala ya bayyana shi.

Ɗanƙarami na aiwatar da tasa sana’ar ce a yankin Gidan Jaja da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi wadda ke da iyaka da Jihar Katsina.

“A gabashin Gidan Jaja, Ɗanƙarami aka sani. A da yana aiki da Hassan da Hussaini ‘yan tagwaye kafin a kashe su.”

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.