fbpx
Sunday, August 7
Shadow

Bayan fitowa takarar shugaban kasa, An ga Fastocin Osinbajo dake cewa shi butule, maciyin Amana

Fastocin dake cewa Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo butulu ne kuma maciyin amana sun cika babban birnin tarayya, Abuja.

 

Fastar tace Osinbajo yaci amanar me gidansa inda aka rubuta cewa ya tuba.

 

Osinbajo dai ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa inda hakan yasa magoya bayan Tinubu ke cewa yaci amanar Tinubun.

 

Ko da shi Tinubun da aka tambayeshi, ya nuna alamar tsayawa takarar shugaban kasar ta Osinbajo bata masa dadi ba.

 

Inda akace me zaice akan tsayawar dansa takarar shugaban kasa? Sai ya kada baki yace shi fa bai da da.

Leave a Reply

Your email address will not be published.