Shugabanni suna ta kokarin haramta almajiranci da bara a arewacin Nigeria musamman a dalilin zuwan wannan cuta na Coronavirus, har ma ana cewa Almajirai suna yada cutar Coronavirus, amma ba mu ga wani yunkuri da sukeyi na daukar mataki a kan Karuwai da gidajen karuwai ba.
Muna goyon bayan a haramta bara dari bisa dari, domin bara baya daga cikin tsarin karantarwan Musulunci, bara kaskanci ne, amma bama goyon a hana Almajiranci, ayi doka duk wanda zai tura yaranso Almajiranci to ya dauki nauyin cinsa da shansa da sutura, Almajirin da akaga yana bara a kamashi a kuma rufe tsangayar da yake karatu.
Kuma muna jawo hankalin masu iko yadda ake ta kwashe almajirai daga jihohi ana mayar dasu inda suka fito ya kamata a haramta karuwanci a rufe duk wani gidan karuwai, sannan duk wata shegiyar karuwa to koma inda ta fito.
Gidan karuwai shima guri ne da ake zuwa a kwaso cututtuka, kuma zai iya zama cibiyar yada cututtuka, saboda a dare daya akwai karuwan da tana yin jima’i da maza dabam-dabam gwargwadon yadda tayi kasuwa, mai Coronavirus zai iya zuwa ya kwanta da karuwa wanda bai dashi idan yazo ya kwashi cutar a jikinta.
Indai ba’a dauki mataki a gidan karuwai ba to mun san fada ake da addinin Musulunci ta karkashin kasa.
Daga Datti Assalafiy
Allah Ka bawa shugabanni ikon yin adalci. Amin