fbpx
Saturday, August 13
Shadow

Bayan kin Tinubu, Kiristocin Arewacin Najeriya sun bayyana cewa ba zasu zabi Atiku ba

Kiristocin arewacin Najeriya sun bayyana cewa ba zasu zabi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ba, wato Atiku Abubakar.

Shugaban VON dan jam’iyyar APC, Mr Osita Okechukwu ne ya bayyana hakan a yau ranar lahadi yayin da yake ganawa da manema labarai babban birnin tarayy Abuja.

Inda yace Kiristocin Arewa basa son tsohon mataimakin shugaban kasar wato Atiku domin basu aminta dashi ba kuma sun san cewa ba zai kawo masu wani cigaba ba.

A kwanakin baya Kiristocin sun bayyana cewa ba zasu zabi Tinubu ba, amm shi yace koda Tinubu yayi nasara ba zasu wahala ba kamar yanzu domin su dama Yarabawa suna yin bikin Sallah da kuma Kiristmeti bakidaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published.