fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Bayan kisan mutane 200, Shugaba Buhari yace ‘yan Zamfara su yi hakuri zai gama da ‘yan Bindiga

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna damuwa da kashe mutanen da ‘yan Bindiga suka yi a jihar Zamfara.

 

Sabon harin da ya faru a Anka da Bukkuyum ya lakume rayuka 200 amma gwamnan jihar, Bello Matawalle yace mutane 36 ne kawai aka kashe.

 

A sanarwar da kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar a madadin shugaban kasar, ya sha Alwashin gamawa da ‘yan Bindigar gaba dayansu.

 

Shugaban ya kara da cewa ba zai taba juyawa ‘yan Najeriya baya ba akan matsalar da suke fuskanta kuma yace ‘yan Bindigar nan zasu zama tarihi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.