fbpx
Thursday, August 11
Shadow

Bayan kisan mutane 38, ‘yan Bindiga sun kuma kashe basarake a Giwa, Kaduna

An kashe Magajin Garin Idosu, da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, yayin harin da yan bindiga suka kai jiya Lahadi.

Wannan na zuwa ne awanni 28 bayan kisan mutane 38 a fadin jihar Kaduna da ƴan bindigar suka yi.

Wani mazaunin ƙauyen Rahiya, inda garin na Idosu yake, ya shaida wa Daily Trust cewa aƙalla kashi 70 cikin 100 na ƴan garin sun watse, yawancinsu sun nufi shalkwatar ƙaramar hukumar ta Giwa, yayin da wasu ke tare da ƴan uwa da abokan arziƙi a Zaria.

Karanta wannan  Mai kudin Duniya, Elon Musk ya sayar da hannun jarinsa na dala biliyan 6.9 na kamfanin Telsa, shin ko meye dalili?

An ce an kashe shi ne lokacin da ya fito neman ɗaukin jama’a yayin da yan bindigar suka yi wa garin tsinke.

Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, inda ƴan bindiga ke kai hare-hare ƙauyuka suna satar jama’a.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.