fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Bayan kisan sojoji sama da 20 da ‘yan Bindiga suka yi a jihar Naija, an kai motar sojoji 10 dan su farauto maharan

A jiyane dai aka tashi da labari mara dadi inda ‘yan Bindiga suka shiga gundumar Erena suka kashe sojoji da dama.

 

Sun kuma kashe farar hula da kuma kama wasu ‘yan kasar China.

 

Saidai dan dakile da kuma nemo wadannan maharan, gwamnatin tarayya ta kai motocin sojoji 10 yankin.

 

Ana tunanin dai Dogo Gide ne da tawagar maharansa da suka kai su 250 suka kai wannan mummunan harin.

 

Wasu rahotannin dai sun ce ana ci gaba da kai gawarwakin wadanda suka mutu Asibitin IBB. Wasu shaidu sun ce wadanda suka mutu sun kai 30 sannan akwai babban jami’in soja cikin wadanda aka kashe din.

Leave a Reply

Your email address will not be published.