by Abubakar Saddiq
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka NCDC ta sake fidda sanarwar kara samun adadin mutum 561 wanda suka harbu da cutar coronavirus a fadin kasar.
Sanarwar wanda hukumar ta wallafa ta cikin shafinta dake kafar sadarwa a ranar talata 30 ga watan Yunin shekara ta 2020.
Haka zalika hukumar ta zayyana jahohin da aka samu karin masu cutar wadanda suka hada da:
Lagos-200 Edo-119 Kaduna-52 FCT-52 Niger-32 Ogun-19 Ondo-16 Imo-14 Plateau-11 Abia-8 Oyo-8 Bayelsa-7 Katsina-6 Kano-5 Bauchi-3 Osun-3 Kebbi-3 Borno-2 Jigawa-1
Bayan haka cibiyar ta bada rahoton sallamar adadin mutum 9,746 sannan kuma an samu.mutuwar mutum 590 a fadin kasar