fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Bayan samun karin masu cutar coronavirus mafi yawa 681 yanzu adadin wanda suka harbu da cutar a Najeriya ya kai 14,554

Cibiyar dakile yaduwar cututtuka wato NCDC ta fitar da sanarwar Samun karin masu cutar coronavirus mafi yawa a kasar.

Cibiyar ce ta sanar da samun Karin mutum 681 wanda ya zuwa yanzu ya kawo adadin masu cutar ya kai 14,554.

A jaddawalin da cibiyar ta bayar na jahohin da aka samu Karin sun hada da.

Lagos-345 Rivers-51 Ogun-48 Gombe-47 Oyo-36 Imo-31 Delta-28 Kano-23 Bauchi-18 Edo-12 Katsina-12 Kaduna-9 Anambra-7 Jigawa-5 Kebbi-4 Ondo-4 Nasarawa-1.

Ya zuwa yanzu an sallami akala mutum 4,494 aka sallama inda mutum  387 suka mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published.