fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Bayan saukeshi daga mukaminshi, APC na shirin korar Adams Oshiomhole kwata-kwata daga jam’iyyar

Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar APC a shirye take ta kori tsohon shugaban ta, Adams Oshiomhole daga cikinta kwata-kwata bayan da ya rasa mukaminshi na shugaban jam’iyyar.

 

Kwamitin gudanarwar jam’iyyar da yayi taronshi na farko karkashin shugaban jam’iyyar na riko, Victor Giadom a fadar shugaban kasa, bisa jagorancin shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya rushe kwamitin gudanarwa na Adams Oshiomhole me membobi 18.

Wannan dalili ne yasa bangaren dake goyo  bayan Oshiomhole yayi barazanar zuwa kotu saboda wannan mataki.

 

Rahotanni dai sun bayyana cewa shugaba Buharine ya bada shawarar rushe kwamitin na Adams Oshiomhole,  kamar yanda hadimin shugaban, Bashir Ahmad ya bayyana.

 

Wata majiya a jam’iyyar ta bayyanawa Punch cewa wannan mataki da bangaren Oshiomhole ke shirin dauka kamar inkarin shugaban kasa ne, kuma kowa yasan cewa inkarin shugaban kasa a jam’iyya me mulki ba abune da zai kare da kyau ba.

 

Majiyar ta bayyana cewa shugaban a lokacin zaman majalisar gudanarwar jam’iyyar yayi gargadin cewa duk wanda yake inkarin jam’iyyar to zai dandana kudarsa kuma ba da wasa yake ba.

Karanta wannan  Zan iya rantsuwa da alkur'ani cewa Atiku ne ya lashe zaben shekarar 2019, cewar Buba Galadimar

 

Daya daga cikin wanda basa tare da Oshiomhole,  Salihu Lukeman wanda shune daraktan kungiyar gwamnonin APC ya bayyana cewa ya kamata kada jam’iyyar ta yi wata-wata wajan korar bangaren su Oshiomhole muddin suka kai jam’iyyar kotu.

 

Yace jam’iyyar ta yi amfani da dokarta me lamba 21 V wadda ta tanadi korar dan jam’iyyar muddin ya kaita ko wani membanta kotu.

 

Dokar dai tace idan dan jam’iyyar na da matsala da ita ko kuma wani membanta to sai ya bi dukkan wata hanyar sulhu da ake da ita ta ki aiki sannanne aka yadda yaje kotu amma idan ba haka ba yana kai karar kotu to za’a koreshi daga jam’iyyar har sai ya janye wancan kara da ya shigar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.