Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike da ya sha kashi a hannun tsohon Mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP, ya yanke shawarar komawa ya goyawa Bola Ahmad Tinubu baya.
Politics Nigeria ta ruwaito cewa, gwamna Wike zai goyawa Bola Tinubu baya wanda shine ake tsammanin zai lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar APC.
Rahoton yace gwamna Wike ya kullaci sauran wasu gwamnonin yankin kudu maso kudu inda yake zargin sun ci amanarsa.