fbpx
Thursday, December 7
Shadow

Bayan shekaru 2, Kasar Saudiyya ta cire dokar coronavirus, tace kasashen Duniya zasu iya zuwa aikin Hajji

Masarautar kasar Saudiyya ta bayyana cewa mutane Musulmai akalla Miliyan daya ne ake sa ran zasu yi aikin Hajjin bana.

 

Mutanen zasu hada da ‘yan kasar Saudiyyar da kuma ‘yan kasashen waje da zasu je.

 

A shekarar 2020 ne dai kasar ta Saudiyya ta dakatar da ayyukan Hajji na mahajjata daga kasashen waje inda ‘yan kasar Mutane 60,000 kadai ne suka yi aikin Hajjin.

 

Kasar tace za’a bar wadanda suke kasa da shekaru 65 su je aikin Hajjin na Bana.

Talla: Danna nan dan samun gagarumar kyauta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *