fbpx
Monday, August 3
Shadow

Bayan shekaru 20 akan mulki, ‘Yan Kasar Rasha sun amincewa Vladimir Putin ya ci gaba da mulki har shekarar 2036

Zaben raba gardama da aka yi a kasar Rasha ya baiwa shugaban kasar damar ci gaba da Mulkin kasar har nan da zuwa shekarar 2036.

 

An dai gudanar da zabenne a yau inda kuma sakamakon ya nuna cewa da yawan ‘yan kasar sun amincewa Vladimir Putin ya ci gaba da mulki bayan kammala wa’adinsa na yanzu da zai kare a shekarar 2024 har zuwa 2036.

Saidai masu sukar zaben sun ce an yi magudi a zaben.

 

Shekaru 20 kenan Putin na mulkin kasar. Inda a yanzu yake da shekaru 67 wanda kuma a shekarar 2036 zai kai shekaru 83 kenan aka mulki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *