Wata mata Mrs Doris Lavi Wilson ta hifi ‘yan 6, bayan da ta kwashe shekaru 28 babu haihuwa.
A shekaru 6 da suka gabata ma ta haifi ‘yan 2 wanda kuma bata sake haihuwa ba sai a wannan karin.
Ta haifi mata 4, Maza 2 ranar 9 ga watan Fabrairun na shekarar 2021. Tana karamar hukumar Ijaw ne ta jihar Bayelsa.