Shekaru 2 kenan tun bayan zuwan cutar coronavirus da shugaba Buhari ya daina karbar gaisuwar sallah da ‘yan yawon Sallah saboda yanda cutar ke yaduwa da dokokin da aka saka na hana yaduwarta.
Saidai a wannan karin, shugaba Buhari ya amince da karbar ‘yan yawon sallah.
Shugaban zai gana da ‘yan yawon sallah akallah 100 a fadar tasa, kamar yanda sanarwa ta tabbatar.
Kakakin shugaban kasar, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka inda yace sai wanda aka gayyata sannan zai je fadar.
Ya kuma kara da cewa duk wanda zai shiga sai ya saka takunkumin rufe baki da hanci.