Bayanai daga jihar Bauchi a Najeriya, na cewa jam’iyyar PDP a jihar na shirin sake zaben fidda gwanin dan takarar gwamna.
A makon jiya ne aka yi zaben kuma Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim ya lashe. Sai dai daga bisani an ji yana cewa ba zai bai wa gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, wanda ya fadi zaben neman takarar shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi ba.