Kungiyar zakarun kasar Jamus wato Bayern Munich tayi nasarar lallasa Borussia Dortmund 3-2 a wasan Der Klassiker na farlo na suka buga a wannan kakar.

Munich tayi nasarar cin kwallayen ne ta hannun zakarun tan wasan ta wato David Alaba,Lewandowski da kuma Leory Sane, yayin da Marco Reus da Erling Braut Haaland suka taimakawa Dortmund da kwallaye biyu a wasan.
Tauraron dan wasan Bayern, Kimmich ya bar filin wasan cikin hawaye bayan ya samu rauni a gwiwar shi yayin daya yi kokarin kwace kwallo a hannun Haaland.
Sakamakon wasan yasa yanzu Bayern Munich ta koma saman teburin gasar Bundlesliga yayin data wuce RB Leipzig da maki biyu kuma ta wuce Dortmund da Mali uku.