Shugaban sojojin Najeriya, Faruk Yahaya ya bayyana cewa dole su kamu ‘yan bindigar da suka kai hari karamar hukumar Shiroro a jihar Niger.
A ranar alhamis ne ‘ya bindigar suka kai harin inda sukayi garkuwa da ‘yan kasar sin guda huku dake hako gwal da kuma wasu ‘yan kasa Najeriya.
Yayin da kuma suka kashe sojoji da ‘yan sanda masu yawa, amma shugaban Soji yace ba zasu laminta ba domin ya bayar da umurni a nemo ‘yan ta’addan da suka aikata wannan laifin don a hukunta su.
Kuma yace ba zasu taba barinsu su huta ba, ya bayyana hakan ne a babban birnin tafayya Abuja.