Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatinshi bazata ki yin abinda ya kamataba kawai dan wasu su yabeta na dan wani lokaci, yace zasu yi abinda ya kamata dan magance matsalolin dake damun jama’a.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Ya kara da cewa ba zasu bi masu ganin cewa su na musammanneba, amma zasu bayar da dama wadda kowa zai iya amfana da ita, ya kara da cewa kuma yayi amannar cewa mutanen jihar sun san cewa wannan zabi da gwamnati tayi na warware matsaloli ta hanyoyi masu tsauri shine ya kamata kuma domin amfanin sune.
Gwamnatin jihar dai ta sallami wasu malaman makarantar firaimare a jihar su kimanin dubu ashirin da biyu, bayan data shirya musu wata jarabawa amma mafi yawanci basu ciba, abinda ya dauki hankulan mutane sosai, ba a jihar Kaduna kadai ba, harda, harma gaba dayan kasar, bayan nan kuma gwamnatin jihar ta sallami wasu ma’aikatan kananan hukumomi.
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});