fbpx
Thursday, May 26
Shadow

“Bazan taba cin amanar talakawaba wajan yin amfani da damata ta shugaban kasa in biyawa ‘ya’ya ko dangina bukatunsu ba”>>Shugaba Buhari

A wani shirin da gidan talabijin na kasa, NTA a kaice ya watsa, jiya Lahadi, akan rayuwar shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa bazai taba cin amanar ‘yan kasa da suka bashi ba wajan yin amfani da damar da yake da ita ta shugaban kasa wajan biyawa ‘ya’yanshi ko kuma wasu danginshi bukatunsuba.


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Shugaba Buhari ya kara da cewa irin kaunar da talakawa ke mishi ce yasa yake cikin harkokin siyasa.
A cikin shirin an nunamataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo da kuma ministoci da gwamnonin jam’iyyar APC sun magana a akan kyawawan halayen shugaban kasar.
A jawabinshi na karshe, cikin shirin da aka nuna, shugaban kasar ya bayyana cewa yana sallah sau biyar a Kullun kuma yana godewa Allah cikin sallolin nashi bisa yanda ya cusawa ‘yan najeriya amincewa dashi da kuma fahimtarshi da sukayi.
A jawabin mataimakin shugaban kasa, Osinbajo, ya bayyana cewa idan shugaba Buhari ya baka aiki kayi, to baya sa maka baki, yana barinka kayi aikin, matukar dai ya amince dakai cewa zaka iya yin aikin, kuma yana da yawan barkwanci.
Shi kuwa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai cewa yayi, lokacin suna a matsayin jam’iyyar adawa, sukan yi shewa da dariya a dakin zaman shugaban kasar amma yanzu hakan bazai yiyuba.
Bangaren kula da harkar kafafen sadarwa da watsa labarai na fadar shugaban kasarne ya shirya wannan shiri kamar yanda jaridar Daily Trust ta ruwaito.  


(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});

Karanta wannan  Jamus na son a binciki China kan ɗaure Musulmin Uighur

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.