Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad ya bayyana cewa ba zai taba janyewa tsohon shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar takarar shugaban kasa ba.
Gwamnan ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a Channels TV.
Ya fadi hakane a matsayin martani ga tambayarshi da aka yi shin me zai hana ya janyewa Atiku Abubakar, ganin cewa, shine yafi alamar samun nasara.
Sanata Bala yace shin me zai hana shi Atiku Abubakar din ya janye masa?
Yace mutum daya ne zai fito takarar shugaban kasa ya janye masa ba tare da wani sa’insa ba, shine tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.