Wednesday, June 3
Shadow

Bazan taba yafewa wanda suka bata min suna ba>>inji Mutumin da ya fara kamuwa da Coronavirus a Kano

Mutum na farko da hukumomi suka bayyana cewa ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19 a Kano, Kabir Rabiu Dansitta ya bayyana cewa ba zai taba yafewa wanda suka watsa labaran karya akanshi ba.

 

Yace ba gaskiya bane labaran da aka rika watsa wa cewa wai shine da gangan ya riga yawo guri-guri a Kano yana da cutar.

Ya bayyana hakane a hirar da yayi da Dailytrust inda yace saida yayi kwana 12 a Kano sannan ya je yayi gwajin cutar dan haka ta iya yiyuwa ma a Kanon ya dauketa.

 

Yace wasu labaran ma sun rika watsuwa cewa wai yana dawowa daga Amurka a Abuja aka killaceshi, sai ya tsere daga wajan killacewa inda har aka harbeshi da bindiga.

 

Yace ba zai taba yafewa wanda suka kirkiri wannan labari ba sai Allah ya saka masa, yace ya wuce shekaru 70 a Duniya to wane dalili zai sa shi ya je ya yadawa ‘yan uwanshi mutanen Kano cuta?

 

Ya kara da cewa, tun a watan satumba yaje kasar Amurka wanda a lokacin ma cutar Coronavirus/COVID-19 bata bayyana a Duniya ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *