fbpx
Friday, July 1
Shadow

Bene ya rufta da mutane da dama a Legas

Ana ci gaba da aikin ceto a wani bene da ya rushe a Lagos a ranar Asabar.

Benen hawa hudu ya rushe ne a unguwar Alayaki Lane a Lagos, yankin da ake tafka ruwan sama.

Masu aikin ceto sun ce mutane da dama ne benen ya rufta da su, yayin da ake ci gaba da kokarin zakulo masu sauran kwana.

Hukumar agajin gaggawa ta jihar Legas ta ce mutum hudu aka samu gawarsu daga baraguzan ginin, yayin da aka ceto mutum biyar a raye.

Hukumomi sun ce benen da ke yankin Lagos Island bakin teku ya rushe ne, kuma tun da farko kafin benen ya rufta an hana ci gaba da aikin ginin saboda rashin inganci da saba ka’aida.

Karanta wannan  Kalli hotunan wani da aka kama yana saka kayan mata da zargin sata

An yi ikirarin cewa an ci gaba da aikin ginin ne a boye yawanci a cikin dare da kuma karshen mako lokacin da ba a aiki.

Matsalar ruftawar gini ba sabon abu ba ne musamman a Legas cibiyar kasuwancin Najeriya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.