A shekaru da dama Benzema yana sadaukar da kyautar Pichichi wadda aka baiwa dan wasan daya fi zira kwallaye masu yawa a kasar Sifaniya wa Cristiano Ronaldo da kuma Lionel Messi, amma a wannan kakar ya shirya lashe kyautar bayan ya zamo dan wasan dan wasan mafi zura kwallaye masu yawa a gasar La Liga.
Real Madrid ta dade tana neman dan wasan da zai maye gurbin Cristiano Ronaldo tun bayan komawar shi Juventus, amma yanzu tauraron dan wasanta na kasar Faransa ya maye gubin nashi yayin da yaci kwallaye 8 a gasar La Liga kuna yaci hudu a gasar Champions League.
Wani abun burgewa shine Benzema ba shine dan wasan daya ke bugawa Madrid bugun daga kai sai gola ba, kawai sai dai yana bugawa ne a lokutan da aka buaci hakan kuma bai taba bararwa ba inda yaci 11 a ganadaya 11 daya bugawa kungiyar.