Tauraron dan kwallon kasar Faransa me bugawa kungiyar Real Madrid wasa, Karim Benzema ya zama dan wasan kasar na farko da ya ci kwallaye 10 a gasar Champions League 1.
Hakanan Benzema ya zama dan wasan kwallon kafa na 2 da yaci kwallaye 3 a wasanni 2 na gasar Champions League a jere bayan Cristiano Ronaldo.
Hakanan shine dan wasa na 4 da ya ci kwallaye 80 a gasar Champions League.
Sannan shine na 4 da yafi yawan kwallaye 3 a wasa daya a gasar Champions League.