fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Benzema ya zamo dan wasa na biyar a cikin jerin sunayen yan wasan da suka fi cin kwallaye masu yawa a kungiyar Madrid

Daren jiya ya faranta ran kungiyar Real Madrid sosai saboda nasarar da suka yi a wasan da suka buga tsakanin su da Valencia har 3-0, wanda hakan yasa suka cigaba da fafatawa da Barcelona a saman teburin gasar La Liga yayin da Barca suka wuce su da maki biyu kacal.

Marco Asensio yayi nasarar cin kwallo daya a daren jiya bayan ya warke daga raunin daya ke fama da shi har na tsawon watannin 11. Shima Karim Banzema yayi nasarar zira kwallaye har guda biyu a daren jiyan.
Kwallon da Benzema yaci ta biyu tasa ya kerewa Ferenc Puskas kuma ya zamo dan wasa na biyar a cikin jerin sunayen yan wasan da suka fi sauran yan wasan kungiyar Madrid cin kwallaye masu yawa, yayin da kwallayen nashi suka kai 243.
Benzema ya shiga kungiyar Real Madrid yana dan shekara 21 a shekara ta 2009 daga kungiyar Olympique Lyonnaise. Kuma bayan shekaru 11 ya zamo dan wasa na biyar a cikin jerin sunayen yan wasan da suka fi cin kwallaye masu yawa a babbar kungiyar La Liga kuma zakarun gasar nahiyar turai.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Karanta wannan  Da Dumi Duminsa: Elon Musk zai saya kungiyar Manchester United

Leave a Reply

Your email address will not be published.