Wani matashi manomi dake kauyen Jeda a baban birnin tarayya Abuja, Hussaini Aliyu daya bace tun ranar Alhamis tara ga wannan watan ya bayyana a mace.
Inda aka gan shi a cikin wata rijiya dake kusa da gonarsa cikin buhu a mace. Wani bawan Allah ya bayyana cewa wasu yara ne dake aiki a gonarsa suka kashe babu dalili.
Kuma suka sace masa raguna 36 da akuyoyi shida bayan sun kashe shi, sannan an dade ana nemansa ba a ganshi ba gar saida jami’an tsaro suka gano shi a cikin rijiya