fbpx
Tuesday, August 9
Shadow

Bidiyo: Allah ne kadai zai gaya mana yanda zamu bauta masa>>Inji Faston kasar Amurka yayin da ya kekketa takardar da hukumomi suka aika masa cewa ya daina zuwa coci

Wani fasto a kasar Amurka ya kekketa takardar da hukumomi suka aika masa inda aka ce ya daina zuwa coci yana tara mutane.

 

Faston dake Baltimore a Maryland, Stacey Shiflett dake jagorantar Ibada a Calvary Baptist church ya bude coci kuma jama’a da dama suka taru ranar Larabar data gabata duk da umarnin da gwamnan jihar, Larry Hogan ya bayar na cewa guraren ibada su bude amma kada a cika su a rika saka mutane rabin yanda ake sakawa a baya.

Shima dai maganin garin Baltimore ya saka dokar cewa kada a tara mutane sama da 10 a wajan ibada.

 

Fastor Shiflett ya bayyana cewa an aika masa da tarar dala Dubu 5. Saidai duk da haka ya sake bude cocin nasa inda ya tara mutane ya kekketa takardar tarar a gabansu inda yace Allah ne kadai zai gaya musu yanda yake so a masa bauta.

Karanta wannan  An zargi gwamnatin Zulum da biyan malaman makaranta Albashin Naira Dubu 6

 

Yace Allah ne kadai yake bada ka’idojin bauta yanda yake so bayinsa su masa bauta.

 

Yace ko Firauna be gayawa mutane yanda zasu yi bauta ba kuma a lokacin da ake tsammanin dawowar annabi isa kamata yayi a rika samun karuwar yawan coci-coci ba wai raguwarsuba.

 

Ya watsar da yagaggun takardun inda yace hanyar Allah zamu bi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.