Hukumar ‘yansandan jihar Imo tace ta kama wadanda suka kashe Ahmed Gulak shekara daya bayan kisansa.
Wanda aka kama din, Anosike Chimobi dan kimanin shekaru 38 yace ya amsa laifin nasa.
Kakakin ‘yansandan jihar, Micheal Abattam ya tabbatar da kamen da aka yi.
