Zanga-zanga ta barke a Kano kan rikicin sarautar da ya faru a jihar.
An ga wasu matasa dauke da kwalaye inda suke ihun basa so.
An kuma ga an kunnawa taya wuta a karkashin wata fastar Abba da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu.
Daily Trust ta wallafa bidiyon wanda ya nuna abinda ke faruwa.
A wani bidiyon kuma an ga matasan na kabbara:
Jaridar dai tace matasan dake zanga-zanga suna neman a sake dawo da Sarki, Aminu Ado Bayero ne kan karagar Mulkin Kano:
Lamari dai ya kazancene bayan da Aminu Ado Bayero ya dawo Kano kuma ya sauka a gidan sarki dake Nasarawa.