Gwamnan jihar Kogi, Yahaya ya bayyana cewa tsohon ministan Sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode ya koma jam’iyyar APC.
Ya bayyana hakane a wani bidiyo da jaridar Independent ta wallafa inda aka ji yana fadar hakan.
A baya dai Femi Fani Kayode ya ziyarci gwamnan sannan kuma ya ziyarci mukaddashin shugaban APC, Gwamna Mai Mala Buni.