Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram ta fitar da wasu bidiyo da hotuna kan yanda ta kaiwa jami’an tsaron Najeriya munanan hare-hare.
Kungiyar ta nuna yanda ya rika yiwa jami’an tsaron ruwan bamabamai da rokoki wanda ya kai ga ta kwace wani sansaninsu sannan ta kwashi makamai da kayan aikin sojojin.
A daya daga cikin hotunan me cike da ban tausai, an ga wani soja na tserewa yayin da ‘yan ‘yan Boko Haram din suka daukeshi hoto.
Hakanan an kuma ga wani dansanda shima yana tserewa da Bindigar sa a hannu wanda shima ga dukkan alama sun kasheshi.
Wani abin mamaki da kuma ban tsoro shine Kungiyar ta nuna yanda ta yi amfani da jirgin sama marar matuki da ake kira da Drone a turance wajan tattara bayanai akan sansanin sojojin kamin ta afkamai.
Hakanan kuma kungiyar ta nuna yanda ta kashe wasu mutane data kama.
Hakan na kara nuni da cewa lallai kungiyar na samun kwarewa wajan kaddamar da ayyukanta, wanda kalubalene ga hukumomi su tashi tsaye.
Domin kallon hotuna da bidiyon faruwar lamarin sai a shiga link din kasa.