fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Bidiyo: Fashewar Wani Abu a Birnin Beirut na kasar Lebanon ya tsorata Duniya: Mutane a kalla 73 sun mutu sama da Dubu 3 sun jikkata

A yaune Duniya ta kadu sosai da ganin fashewar wani bu a Birnin Beirut na kasar Lebanon inda da farko wata euta ta fara ci amma daga baya ta fashe inda ta bazu zuwa gurare da dama.

 

Lamarin ya farune a gabar teku dake birnin, a cikin bidiyo da dama da suka bayyana a shafukan sada zumunta an ga yanda abin me matukar ban tsoro ya faru.

 

Gargadi(Idan kana da sarin Fargaba kada ka kalli wadannan Bidiyo, dan suna da firgitarwa).

 

Ministan harkokin cikin gida na kasar, Mohammed Fahmi yace ana zargin wani kyamikal ne da aka ajiye a wani guri ya kawo fashewar.

 

Hukumomi sun bayyana cewa akalla mutane 73 suka mutu, yayin da sama da Dubu 3 suka jikkata, an rika ganin gawarwakin mutane yashe a kasa, a bidiyoyin da zaku gani a kasa.

 

Hakanan akwai abubuwan ban tausai da firgitarwa dangane da wannan Lamari. Tuni kasar ta bayyana birnin a matsayin wajan da wata Annoba ta barke. Kuma Amurka ta yi tayin bata agaji wajan aikin ceto.

 

 

Wannan wani biki ne da dole aka dakatar da yinsa yayin da lamarin ya faru.

 

Bidiyon kasa, Mutanene ke aikin Agajin ceto.

Wannan Bidiyon ya nuna ainahin yanda lamarin ya faru.

 

 

Bidiyon kasa ya nuna yanda wani me mota dake daukar lamarin daga nesa abin ya shafeshi:

Karanta wannan  Tekun Legas ya tafi da dalibai hudu da suka je murna bayan sun lashe jarabawar WAEC

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.