Wani gawurtaccen dan bindiga da aka kama me sunan Buba Bargu ya bayyana cewa idan an kamasu suna da manyansu da suke kiran lauyoyi su basu kudi a sakesu.
Ya bayyana hakane a hirar da jami’an tsaro suka yi dashi bayan kamashi ana shirin gabatar dashi a gaban kuliya.
Hutudole ya Fahimci Bargu na da yaransa kuma yana daga cikin wanda suke kai hare-hare a hanyar Lokoja da yankunan dake kusa da wajan. Yayi bayanin yanda suke samu makamai da kuma irin yanda Boko Haram ke kama mutane suna kashesu.
Kalli Bidiyon a kasa: