fbpx
Tuesday, July 5
Shadow

Bidiyo: Gwamnan Najeriya ya fashe da kuka saboda Tausayin Talakawa, Yace kada a kara karbar haraji a hannun talakan jiharsa

Gwamnan jihar Cross-River,  Ben Ayade ya bayyana takaicinsa kan halin da talakawa ke ciki a jiharsa inda yace ya kusa fashewa da kuka bayan da yaga cewa shekaru 5 kenan yana mulki amma har yanzu a jiharsa akwai mutane dake zama a gidan kasa.

 

Gwamnan yace idan da Allah zai kwace duk abinda ya mallaka dan kowane dan jiharsa ya samu Arziki to zai so hakan.

Gwamnan ya fashe da kuka saboda tausayin talakawa inda yace kada a kara karbar haraji a hannun duk wani talaka da karamin dan kasuwa, ciki hadda otal-otal dake da dakuna kasa da 50 a jihar.

 

Gwamna Ben Ayade ya bayyana hakane a yayin da yake kaddamar da kwamitin yaki da karbar haraji a gurin talaka.

 

Yace yana fatan kwamitin zai yi aiki yanda ya kamata, inda yace ta yaya gwamnati bata yiwa talakawa abinda ya kamata a gurare da yawa ba amma kuma mutum yayi wahalarshi ya samo kudi kuma ace wai sai ya biya Haraji?

Karanta wannan  Kungiyar magoya bayan Tinubu ta bayar da shawarar ya dauki Gwamna Elrufai a matsayin mataimakinsa

 

Kalli bidiyon gwamnan yana kuka a kasa:

Wannan abu ya jawowa gwamnan Yabo sosai musamman a shafukan sada zumunta inda akai ta bayyana mamakin cewa dana akwai shuwagabanni irin haka?

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.