Tauraron fina-finan Hausa, Saddiq Sani Saddiq ya bayyana cewa yana tausayawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari saboda yasan sai Allah ya tambayeshi yanda yayi mulkinsa.
Saddiq a sakon da ya fitar ta shafinsa na Instagram ya bayyana cewa shugabannin Najeriya sun rantse da kur’ani kan cewa zasu kare ‘yan kasa amma ga abin yafi karfinsu, Musamman ma Shugaban kaaa, Muhammadu Buhari.
Ya kara da cewa Azzalumai sun zagaye shugaban kasar sun hana malamai su rabeshi su gayamai gaskiya. Yace tabbas yana tausayawa shugaban kasar saboda yasan sai Allah ya tambayeshi yanda ya gudanar da mulkinsa.
https://www.instagram.com/p/CITDwgjnPzo/?igshid=1f5d7hqtm8l4b