Babban lauyan gwamnati kuma ministan shari’a, Abubakar Malami na shan caccaka kwanannan saboda rabawa mabiyansa da masu goyon bayansa a jihar Kebbi motocin Alfarma.
Malami na neman tsayawa takarar gwamnan jihar Kebbi karkashin jam’iyyar APC.
A baya dai da maganar raba motocin ta fito, Malami ya karyatata.
Saidai a yanzu wani Bidiyo ya bayyana inda yake alfahari da raba motocin.
An jishi yana fadar cewa wasu ‘yan Adawa sun ce raba motoci 200, yace to idan jirgin sama ne Allah ya hore masa zai raba.
Wasu dai dake sukar wannan maganar raba motocin na tambayar shin a ina Abubakar Malami ya samo kudin da ya sayi motocin.
Attorney-General Abubakar Malami is seen here bragging about sharing 200 exotic cars worth over N2.7 billion last week. He also hopes to share airplanes.
Months before he was appointed in 2015, Mr Malami told a Kano radio he couldn't afford N12 million to renovate his residence. pic.twitter.com/hnTOKXoPcR
— Peoples Gazette (@GazetteNGR) May 7, 2022
Motocin da aka gani hotunansu na yawo a shafukan sada zumunta wanda Rahotanni suka nuna cewa sune malami ya raba, sun hada da marsandi kirar GLK, da Prado da sauransu.


A shekarar 2015 dai kamin a bashi mukamin ministan shari’a, Abubakar Malami ya taba gayawa wani gidan rediyon Kano cewa bai da Miliyan 12 da zai gyara gidansa, kamar yansa Peoplesgazette ta ruwaito.