fbpx
Friday, July 1
Shadow

Bidiyo: Ma’aikatan Majalisar Dokoki (NASS) sun tare babbar kofar shiga harbar majalisar yayin da suke zanga-zangar rashin biyan albashi da alawus

Ma’aikatan Majalisar Tarayya da Hukumar Kula da Ma’aikata ta Kasa, sun tare babbar hanyar shiga harabar majalisar a yayin da suke zanga-zangar kin biyan alawus-alawus da albashi.

Ma’aikatan a karkashin inuwar kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin Najeriya (PASAN) sun yi gargadin a ranar Juma’a 3 ga watan Yuni, za su fara yajin aiki na dindindin a ranar Litinin 6 ga watan Yuni.

Sun zargi mahukuntan majalisar dokokin kasar da yin watsi da yarjejeniyar fahimtar juna don aiwatar da cikakken tsarin aikin da aka yi wa kwaskwarima da horas da ma’aikata.

Karanta wannan  Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kashe wasu sojoji da ba a tantance adadinsu ba a Jihar Neja

Suna kuma neman a biya su basussukan mafi karancin albashi, tallafin hutu da sauran alawus-alawus

Duba bidiyon a kasa….

https://www.instagram.com/tv/CedgXktAt6J/?igshid=YmMyMTA2M2Y=

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.