Mutane a karamar Birnin Gwari sun fito zanga-zanga kan matsalar tsaro dake addabar yankin inda suke neman hukumomi su tallafa a shawo kan matsalar.
Mata da kananan yara, musamman wands aka kashe mazajensu ne ke dauke da kwalaye masu rubuce-rubuce dake neman a kawo karshen matsalar tsaron.
Wata Murya dake cikin Bidiyon ta yi bayanin cewa, zanga-zangar lumanace dan kira ga hukumomi a dauki mataki akan lamarin in baka ba ‘yan Bindiga zasu kawar da karamar hukumar Birnin gwari daga doron kasa.