fbpx
Thursday, August 18
Shadow

Bidiyo: Yanda SARS suka ci zarafina duk da mukamina>>Kanal din soja ya bada Labari

Tsohon sojan Najeriya me mukamin Kanal, Hassan Stan-Labo ya bayyana yanda ‘yansandan SARS suka ci zarafinsa a yayin da yake tare da iyalansa a Mota.

 

Ya fadi haka a wata hira da aka yi dashi a gidan talabijin na Arise TV inda yace sai ka ji ma’aikacin SARS yace maka sai in kashe ka kuma babu abinda zai faru.

 

Yace kuma da gaskene saboda SARS nawa ne shugaban ‘yansanda, IGP Muhammad Adamu ya hukunta saboda cin zarafin mutane?

 

Yace sun tsayar dashi yana tare da iyalansa amma bai gaya musu ko wanene shi ba, yace da suka fara wuce gona da iri sai suka gano cewa shi soja ne, yace amma duk da haka wai sai suke tambayarsa me zai basu.

Karanta wannan  Tekun Legas ya tafi da dalibai hudu da suka je murna bayan sun lashe jarabawar WAEC

 

Yace ya kallesu yace direbana ba zai wa oganka haka ba kuma ban zarge ka ba, irin horon da ka samu kenan. Yace matarsa ce tacs masa me gida mu je fa saboda mutuminnan na rike da bindiga ne kada ayi abinda ba dadi, yace kuma dole ya saurari matar tasa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published.