Tun bayan da Tauraron mawakin Siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana neman tallafin Naira Dubu-Dubu daga hannun masoya shugaban kasa, Muhammadu Buhari da yiwa shugaban kasar waka, hankula suka koma kan wannan lamari sosai.
Ya zuwa yanzu dai masoyan shugaban kasar da dama nata turawa Rarara tarin kudi da dama dan ya rerawa gwanin nasu waka.
A wani Rahoto da Kannywood exclusive ta ruwaito tace wata majiya ta gaya mata cewa Biliyan 2 Rarara ke son tarawa daga masoyan shugaban kasar kamin ya fara waka. Saidai zuwa yanzu babu rahoto kan nawa mawakin ya tara.