fbpx
Wednesday, August 10
Shadow

Bidiyo:Dakarun Sojojin Najeriya sun lalata maboyar Boko Haram tare da halaka da dama

Dakarun sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram da dama tare da lalata maboyarsu a yankin Warshale dake Arewacin Borno.

 

Rahoton da hedikwatar tsaron Najeriya ta fitar ya bayyana cewa, sojojin sun samu bayanan sirri inda suka kuma tabbatar dasu.

 

Tace daga nanne sai aka tashi jiragen yaki inda suka je suka yi ruwan bama-bamai akan maboyar ta Boko Haram inda suka lalatata da kuma kashe da dama daga cikin mayakan.

 

Sanarwar ta kara da cewa shugaban Sojin, AVM Sadiq Abubakar ya jinjinawa sojojin bisa wannan nasara inda ya bukaci da su kara kaimi.

Leave a Reply

Your email address will not be published.