Hadikwatar tsaro ta kasa ta bayyana cewa sojojin Saman Najeriya dake rundunar Operation Lafiya Dole sun kaiwa mayakan Boko Haram hari a garin Parisu dake jihar Borno.
Mayakan na Boko Haram da yawa sun halaka a harin inda kuma aka lalata kayansu da rusa musu gine-gine.
Hakan na zuwane bayan samun bayanan Sirri akan kungiyar dake cewa sun taru suna shirin kaiwa sojojin hari.
Kalli bidiyon yanda harin ya kasance.
AIR TASK FORCE OF OPERATION LAFIYA DOLE KILLS SEVERAL TERRORISTS, DESTROYS THEIR LOGISTICS FACILITIES IN AIR STRIKES AT PARISU, BORNO STATE https://t.co/LNhAWp8nfE pic.twitter.com/LKH5honI0I
— DEFENCE HQ NIGERIA (@DefenceInfoNG) May 1, 2020
An yi bincike kuma an tabbatar da haka, kamar yanda sanarwar ta bayyana, daga nanne sai rundunar ta sojin sama ta aika jiragenta suka yi ruwan bama-bamai akan ‘yan ta’addar.