Sunday, May 31
Shadow

Bidiyo:Motar Mayakan Boko Haram na ci da wuta bayan Luguden bama-bamai da Sojojin Najeriya suka mata

Wannan bidiyon motar mayakan Boko Haram ne take ci da wuta a wani harin kwantan bauna da sojojin Najeriya suka kaiwa Boko Haram din suka kashe 9 daga cikinsu.

A karshen makon daya gabatane sojojin Najeriya suka kaiwa Boko Haram din harin kwantan bauna a Mainok yayin da suke kan hanyarsu ta kaiwa wasu kauyuka hari.

 

Sojojin sun kashe 9 daga cikin Boko Haram din inda suka kuma kwace wasu daga cikin makaman Boko Haram din.

Shugaban Sojin Najeriya, Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa ya koma yankin Arewa maso gabas da zama inda sai bayan an kammala da Boko Haram zai koma Abuja.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=hdlabarai.aplibwxLeave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *