fbpx
Monday, January 18
Shadow

Bidiyon Boko Haram na gudun tsira yayin da Sojojin Najeriya ke musu ruwan Bama-bamai

Sojojin Najeriya sun sanar da fatattakar Boko Haram a wani hari da suka kai musu ta jirgin yaki a Mainok jihar Borno.

 

Hedikwatar tsaron Najeriya ta wallafa Bidiyon jirgin yakin Sojojin inda ya hango motocjn yakin Boko Haram suna tafiya.

 

Koda Boko Haram din suka hangi jirgin yakin sai suka fara fita daga cikin Motocin yakin nasu suna gudun tsira amma tuni jirgin ya rika musu ruwan bama-bamai.

 

Rundunar Tura ta kai Bango ta sojojin Najeriya na kai hare-hare a ‘yan kwanakinnan babu kakkautawa akan Boko Haram dan ganin cewa an gama da Kungiyar.

 

Kalli Bidiyon a kasa.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *