Tauraruwar fina-finan Hausa,Rahama Sadau kenan a wannan kayataccen Bidiyon nata inda take rausayawa.
Sadau ta saka Bidiyon a shafin ta na sada zumunta inda aka ga ana daukar ta hotuna.
https://www.instagram.com/p/CLgjOZfhLU4/?igshid=1vjl5h0oyrykk
Hakanan ta saka wasu hotuna masu daukar hankali saidai a wannan karin bata bada damar ayi Comment ba saboda karma wani ya fadi maganar da bata dace ba.
A baya dai Rahama Sadau ta saka wasu hotuna da suka nuna gadon bayanta wanda har suka kai ga an yiwa fiyayyen Halitta batanci akansu wanda hakan yasa akai ta Allah wadai da lamarin.
Saidai a wancan karin Sadau ta fito ta bada hakuri inda tace badan a yiwa Annabi(SAW) batanci ta saka hoton ba, Sadau har kuka ta yi tace ta daina.
A wancan karin Ali Nuhu, Adam A. Zango duk sun nesanta kansu da Rahama Sadau akan wanacan lamari inda kuma aka kara samun wasu jarumai da suka rufa musu baya.