Majalisar Dinkin Duniya, MDD ta bayyana cewa ta gano tare kuma da dakatar da ma’aikatanta 2 da bidiyonsu ya watsu sosai suna lalata a cikin motar majalisar.
Lamarin ya farune a Tel aviv, Kasar Israel inda aka dauki bidiyon motar majalisar Dinkin Duniyan dake tafiya da mutane 2 a gaba, Direba da wani a wajan zaman fasinja da kuma wani mutum a bayan motar, wata farar Mata na zaune akan cinyarsa.
Bidiyon ya bayyana a makon jiya. Da yake fitar da sanarwa akan lamarin, Kakakin sakataren majalisar, Stephane Dujarric a jiya,Alhamis ya bayyana cewa an dakatar da wanda ake zargi inda aka ce su tafi hutun da ba biyan Albashi.
Yace majalisar ta kadu sosai da jin wannan lamari inda yace ana kan bincike dan sanin mataki na gaba da ya kamata a dauka.